Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 300 Salama Ta Allah Kamar Kogi Ce Lyrics
1
Salama ta Allah kamar kogi ce.
Tana ikon kome cikin yalwarta.
Cikakkiya mai gudu, tana ƙaruwa,
Cikakkiya mai girma kamar zurfafa.
KORUS
Dogara ga Allah, hanyar kwanciyar rai
Gunsa za a sami hutu cikakke.
2
Daga tafin hannun Ubangijinmu,
Ba abokin gaban da zai fizge mu.
Babu tashin zuciya, babu damuwa,
Babu kuwa dalilin tunani mai yawa.
Korus
