Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 3 Abu Duk A Duniya Ubanmu Ne Ya Yi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 3 Abu Duk A Duniya Ubanmu Ne Ya Yi Lyrics

 

1
Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci.
Shi ya kan ba mu ruwa a loton shukawa,
Har amfanin gonaki ba za mu rasa ba.

2
Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci.
Ya ba mu hasken rana, mu kama aikinmu.
Duhun dare kyautarsa, mu riƙa hutawa.

3
Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci.
Duk masu rai na duniya, ya kan ciyad da su.
Kifaye da tsuntsaye, ya san bukatarsu.

4
Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci
Mu kuma Masu Binsa aikin hannunsa ne, Ubanmu mai ƙauna mahaliccinmu ne.

Exit mobile version