Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 299 Yesu Ne Ya Yiwo Gafara Lyrics
1
Yesu ne ya yiwo gafara
Domin masu zunubi.
Yesu ne ya ba mu sabon rai,
Rai fa na har abada.
KORUS
Akwai murna fa da hutu
Cikin sunan Yesu Mai Ceto
Domin kullum ya ke nan tare da mu.
Ba zai bar mu ba, ko kaɗan.
2
Ga alkawaransa wurinmu,
Za ya cika dukansu.
Ba zai tashi ko ya bar mu ba
Har iyakar zamani.
Korus
3
Za ya biya duk bukatarmu
Domin zaman duniya
Bisa ga wadatar Allahnmu
Cikin Sama, gidansa.
Korus
4
Kome dai da Za mu yi roƙo
Cikin sunan Ɗan Allah,
Allah dai zai cika mana shi
In mun ba da gaskiya.
Korus
5
Sai mu riƙa ba da gaskiya,
Sai mu kau da shakka duk,
Gama Yesu mai aminci ne,
Faɗarsa ta tabbata
Korus