Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 297 Ya Ƙaunar Almasihu, Ban San Iyaka Ba Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 297 Ya Ƙaunar Almasihu, Ban San Iyaka Ba Lyrics

 

1
Ya ƙaunar Almasihu,
Ban san iyaka ba,
Da zurfinta da tsawonta
Sun wuce faɗina.
A gindin giciyen Almasihu
Na zauna, hutun rai na yi.
Rijiyar ƙauna cikakkiya da rai,
Kai ka bayar a shayad da ni.

2
Ya ƙaunar Almasihu
Wadda ta riƙe ni,
Ta bi ni, ina nesa,
Ta kawo ni wurinka.
Ta amshi dukan zuciyata,
Ta sa na zama bawanka.
Duniya duk ta kasa jawo ni,
Domin ikon ƙaunarka.

3
Ya ƙaunar Ubangiji,
Ya zuciyar Allahnmu,
Ga zunubi a duniya,
Ga girman ƙaunarka.
Ga ƙofar rai a buɗe yau,
Ƙauna ta buɗe ta.
Ba mu yin fahariyar kome,
Sai dai giciyen Almasihu.

Exit mobile version