Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 295 Albarkacin Allah ‘Na Zuwa Lyrics
1
Albarkacin Allah ‘na zuwa
Kamar dai a ke yin ruwa
Bisa ga baiwa da bawa,
Bisa kan mutane duk.
KORUS
Albarkacin Allah,
Albarkacin Allah ‘na zuwa
Kamar dai a ke yin ruwa
Bisa kan duniya duk.
2
Albarkacin Yesu ‘na zuwa,
Yadda kuwa Allah ya ce,
Ga wanda ya ba da gaskiya,
Ga wanda ya yarda da shi.
Korus
3
Albarkacin Ruhu Mai Tsarki
Shi kasance tare da mu
Har zukata duka su cika
Da iko da ƙaunar Yesu.
Korus