Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 294 Ga Shaidar Kawar A Tsoro, Ita Ce Giciye Lyrics
1
Ga shaidar kawar a tsoro, ita ce giciye.
Hatimtacce da giciyce, bawan Yesu, ka tsaya.
2
Shaidar ba za ka razana a yaƙin Almasihu,
Ƙarƙashin tutarsa kullum da ƙarfi za ka tsaya.
3
Shaidar kai kuma za ka bi hanyar da ya bi dā,
Jure kunya da giciye, zama mai nasara.
4
A sarari kowa zai ga an hatimce ka dai.
Goshin da ke da giciye, kambin sarauta ne.
