Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 293 Shi Wanda Zai Daure da Duk Wahalai Lyrics
1
Shi wanda zai daure da duk wahalai,
Bari a koyaushe ya bi Shugaba.
Ba zai karaya ba, ko sake nufinsa,
Alkawari ya yi, bin Yesu zai yi.
2
Masu son su ƃad da shi da mugun zance,
Suna cutar kansu, shi gaba zai yi.
Maƙiyi zai kasa, kome dabararsa,
Zai kama hanyarsa, bin Yesu zai yi.
3
Tun da ka kāre mu da Ruhun ƙarfi,
Mun sani mun doshi rai har abada.
Kome zai shuɗe fa, ba zan ji tsoro ba,
Koyaushe nufina, bin Yesu zan yi.