Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 292 Yaƙi Yana Nan Gaba da Shaiɗan Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 292 Yaƙi Yana Nan Gaba da Shaiɗan Lyrics

 

1
Yaki yana nan gaba da Shaiɗan,
Sai ka ƙarfafa cikin Yesu.
Yafa makamai domin iko dai,
Sai ka tsaya kan Maganarsa.

KORUS
Ji, ƴan yaƙi ! Haɗa kai da Kristi!
Tashi, shirya! Ba da shaidarsa!
Ci gaba dai, raira waƙar yabo!
Yesu Kristi Shugabanmu ne.

2
Ga maƙiyanmu, tsoro ba ma ji,
Gaba za mu yi, Ubangiji!
Ɗauki takobi, nuna haskenku,
Yaƙin Yesu sai da nasara.
Korus

3
Ya kai Allahnmu, ji kukanmu dai,
Taimake mu da ƙarfinka,
Yaƙi zai ƙare, za mu tatu can,
Ka karƃe mu cikin hutunka.
Korus

Exit mobile version