Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 291 Su Magauta Dayawa Ne A Kewaye da Mu Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 291 Su Magauta Dayawa Ne A Kewaye da Mu Lyrics

Hymn 291 Su Magauta Dayawa Ne A Kewaye da Mu Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 291 Su Magauta Dayawa Ne A Kewaye da Mu Lyrics

 

1
Su magauta dayawa ne a kewaye da mu.
Shaiɗan da dukan runduna sun zo su kā da mu,
Amma an shirya makamai don wannan yaƙi fa.
A cikin sunan Yesu ne za mu ci nasara.

KORUS
Yesu mai nasara, Yesu mai nasara,
Da sunan Yesu ne mu ke yin nasara.

2
Kwalkwalin ceto bisa kai, ɗamarar gaskiya,
Da garkuwa ta bangaskiya, sulken adalci ma,
Shirin bishara takalmanmu ne a ƙafafu,
Ga takobi na Ruhu ma, wato Maganarsa.
Korus

3
Mu yi addu’a koyaushe, mu yi aniya fa,
Mu yi roƙo da naciya don dukan tsarkaka,
Mu tsaya dai da ƙarfi fa, mu yi tsayayya ma,
A cikin ikon Yesu ne za mu ci nasara.
Korus

Post navigation

Previous: Hymn 116 Ta da Kanku, Ƙyamare, Halleluya Lyrics
Next: Hymn 139 Sai In Ba Ku Labarin Nan, Zance Mai Ba da Rai Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version