Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 289 Sunan Yesu Shi Ne Mafi Ɗaukaka Lyrics
1
Sunan Yesu shi ne mafi ɗaukaka
Cikin dukan sunaye.
Babu wani suna wanda ya isa
Cetonmu, sai shi kaɗai.
KORUS
Yesu ne Mai Ceto,
Ba wani Allah za mu bi,
Cikin sunansa, nasara,
Babu shakka, za mu yi.
2
Yesu ya ci nasara da zunubi,
Ba da ikon duniya ba,
Sai ta wurin mutuwa da tashinsa
Daga cikin kabari.
Korus
3
Halin Almasihu mu ke so mu yi,
Ruhunsa ya cika mu
Don mu shaida shi ga dukan mutane,
Cewa ya yi cetonsu.
Korus
4
Sai mu ƙanƙantad da kanmu, ƴanuwa,
Kamar yadda shi ya yi.
Mu yi nufinsa da farar zuciya,
Har matuka za mu bi.
Korus
