Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 288 Mu Tashi Tsaye, Dukan Ƴan Yakin Giciye Lyrics
1
Mu tashi tsaye, dukan ƴan yakin giciye,
Mu ta da tuta bisa domin a gan ta dai.
A cikin yaƙin gaskiya, Yesu zai bishe mu kuwa
Ba za mu koma ba fa, sai gaba za mu yi.
2
Mu tashi tsaye duka, biyayya za mu yi
Ga Yesu, Shugabanmu, a cikin yaƙinsa.
Ku mazaje ku tashi, ku yi da ƙarfin hali,
Ko tsoro ko ragwanci, ba damar wannan fa!
3
Mu tashi tsaye duka, a cikin ikonsa.
A cikin ikon kanmu, ba za mu isa ba.
Mu tafi da bishara, mu yi ta yin addu’a.
Ta wurin bangaskiya za mu ci nasara.
