Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 286 Shi Yesu Ne Mai Nasara A Bisa Maƙiyi Lyrics
1
Shi Yesu ne Mai Nasara a bisa Maƙiyi.
Tun ran da aka giciye shi, ya ka da zunubi.
Ya gama aiki duk a can, ya kawo gafara, Sai mu mu ba da gaskiya ga Ubangijinmu.
KORUS
Ta wurin bangaskiya na sami nasara,
Ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.
2
Yanzu mu Masu Bill Yesu mun sami gafara.
Kada mu rasa nasara a bisa Makiyi.
Ba za mu bauta wa Shaidan, mu saurare shi ba.
Zunubi ba zai ka da mu, ya kai mu mutuwa ba.
Korus
3
Yesu shi ne mai mulkinmu a cikin duniya,
Mu sa kanmu a hannunsa, mu nemi nufinsa.
Abin da ya ke so mu yi, mu yi da zuciya daya
Don kada zvnubi ya zo, ya rinjaye mu dai.
Korus
