Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 285 Ku Yi Ƙarfin Zuciya Cikin Allahnmu Lyrics
1
Ku yi ƙarfin zuciya cikin Allahnmu.
Shaiɗan da mala’ikunsa sun kewaye mu duk.
KORUS
Sai mu tsaya cikin ikon Yesunmu
Sai mu riƙa ƙaunar Almasihu Mai Ceto.
2
Ga shi, Shaiɗan yana nan cikin duniya,
Yana fushi in ya ga mu bayin Yesu ne.
Korus
3
Kome yawan wahala da Shaiɗan ya kawo,
Sai mu bi Ubangiji, zai ba mu nasara.
Korus
4
Idan muna jurewa zuwa matuƙa,
Almasihu za ya ba mu kambin nasara.
Korus
