Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 284 Ya Almasihu, Sarkin Tsarkakanka Lyrics
1
Ya Almasihu, sarkin tsarkakanka,
Kai ne ka taya su cikin jaraba.
Duk Masu Binka suna yabonka.
Halleluya! Halleluya!
2
Kai ne mazauninmu har abada,
Kai fā na ceto ne da mai taimako.
Kai Shugaba ne cikin yaƙinmu.
Halleluya! Halleluya!
3
Idan da tsoro cikin zukatanmu,
Ko ikon Shaiɗan ne ya ke ƃata rai,
Kai ne ka fi shi, kai kuwa namu ne.
Halleluya! Halleluya!
4
Kai ne ka kira mu mu bi bayanka.
Kai za ka taya mu cikin yaƙin nan.
Shaiɗan, magauci, za ka taka shi.
Halleluya! Halleluya !
5
Sai wata rana sammai za su buɗe,
Za ka bayyana nan cikin daraja.
Mu kuwa magada ne na muikinka.
Halleluya! Halleluya!