Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 281 Yaƙi ‘Na Nan, Yaƙi Na Almasihu Ne Lyrics
1
Yaƙi ‘na nan, yaƙi na Almasihu ne,
Ku Masu Bi, yi shirin yaƙin nan.
Ubangijinmu shi ne sarkin yaƙin nan
Da mu ke yi, zai ba mu nasara.
KORUS
Yaƙi ‘na nan, ku Masu Binsa,
Ku nemo kayan yaƙin nan,
Sulken adalci, kwalkwalin ceto,
Da garkuwa ta bangaskiya,
Takalma na shirin bishara,
Gaskiya ce ɗamararmu,
Takobin Ruhu–Maganar Allah,
Da su mu ke yin nasara.
2
Ku ƙarfafa a cikin Ubangijinmu,
Ku tsaya fa ta wurin bangaskiya.
Kokawarmu tare da Shaiɗan ne da
Ikoki nasa da kuma zunubi.
Korus
3
Ku yi aniya, ga Yesu yana zuwa
Don ya dube mu a cikin yaƙin nan.
Ga shi, hakkinsa yana nan tare da shi,
Zai bayar wa masu cin nasara.
Korus