Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 28 Ku, Za Ku Ina? Lyrics
Ku, za ku ina?
Za mu tafi majami’a, mu yi wa Allah yabo.
Yabon menene?
Domin abinci, rai da sutura da Allah ya ke ba mu.
Wannan kaɗai, ko?
A’a, daa sauran abu da yawa da Allah ya ke ba mu,
Sauran menene?
Saura dayawa, kwanciyar zuciya,
Murna da farinciki
Don me da murna?
Muna murna saboda Yesu ya zo ya kawo ceto.
Kuna biya menene?
Ba mu biya ba, daga alherinsa ya biya laifofinmu.
Ƙaƙa zan samu?
Tuba ka yarda Allah ya aiko Yesu
don ya ceci duniya
Wannan na yarda.
To, ya isa, an cece ka, ka zo mu tafi tare.
Za ni tare.
To mu tafi majami’a mu yi wa Allah yabo.
