Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 278 Mai Ceto Nawa Yesu Ne Lyrics
1
Mai Ceto nawa Yesu ne,
Ga magauta a kewaye,
Ga kuwa jaraba ko’ina,
Amma ba zan ji tsoro ba.
KORUS
Mai Cetona, Mai Cetona
Mai Ceto nawa Yesu ne.
A cikin hannunsa na ke,
Shi kuma yana tsarona,
Mai Cetona, Mai Cetona,
Mai Ceto nawa Yesu ne.
2
Shaiɗan da dukan wayonsa,
Na sani yana nemana,
Amma Mai Cetona ‘na nan,
Ba zan damu ba, ko kaɗan.
Korus
3
Kwatancin Yesu na ke bi,
Maganar Yesu na ke ji.
Shaiɗan ya zo da ruɗinsa,
Ni ba zan kasa kunne ba.
Korus