Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 277 Ina Cikin Yaƙi, Magautana Kuwa Lyrics
1
Ina cikin yaƙi, magautana kuwa
Shaiɗan ne da duniya, duk da zuciyata.
Ubangiji Yesu, ji addu’ata,
Ban da taimakonka sai in halaka.
2
Ni ban isa kome cikin yaƙi ba.
Sai da taimakonka zan ƙori Shaiɗan.
In ka bar ni, Yesu, mutuwa zan yi.
Yesu, na roƙe ka, riƙe ni yanzu.
3
Kowane Mai Binka, in ya kira ka,
Za ka taimake shi cikin yaƙinsa.
In ka ba ni iko, zan yi nasara.
Na roƙe ka, Yesu, kai ni lafiya.