Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 276 Mai Bin Ubanginmu, Ka Kama Hanyarsa Lyrics
1
Mai Bin Ubanginmu, ka kama hanyarsa,
Yesu ne ya ke kira, Yesu ne ladanka.
2
Ka yad da aikin duhu, ka tuƃe zunubi,
Yi tseren nan gabanka tare da haƙuri.
3
Ba za ka ji Shaiɗan ba, ba za ka koma ba.
Tare da Almasihu, bari ka ci gaba.
4
Raini ba za ka ƙi ba, kada ka ji tsoro.
Ka dubi Almasihu, kullum ka shaida shi.
5
Mai Bin Ubangijinmu, ka dubi darajar
Da aka sa gabanka, ka gama lafiya.
