Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 274 Yesu Ni Ne Naka, Zan Bi Ka Kuwa Lyrics
1
Yesu ni ne naka, zan bi ka kuwa,
Tun ka kori duhu daga zuciyata.
Kome yawan duhu nan a duniya,
Inda na ke duka, zan haskaka.
2
Dā, na sha wahala gun magauci,
Har ka wanke zuciya daga zunubi.
Sai ka ƙarfafa ni cikin hanyarka.
Inda na ke duka, zan haskaka.
3
Yesu ni ne naka, zan shaida kuwa,
Don mutanen duniya su ga haskenka.
Raina za ya zama kamar fitila,
Inda na ke duka, zan haskaka .
