Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 273 Ubangijin Girbi ‘Na Kiranmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 273 Ubangijin Girbi ‘Na Kiranmu Lyrics

 

1
Ubangijin girbi ‘na kiranmu.
Ga hatsi ya nuna, mu zo yanzu,
Mu tashi mu je gun ƃattatu,
Mu shaida labarin Mai Cetonmu.

KORUS
“Wa za ya tashi ?” in ji Yesu,
In aike shi a wurin ƃatattu.
“Ya taimake ni da nemansu,
Ya shaida musu akwai ceto.”

2
Ku duba, girbi dayawa ne,
Ga ma’aikam kuwa, kaɗan su ke
Mu yi roƙo gun Ubangiji
Ya aiki manzanni domin su ji.
Korus

3
Ka yi addu’a, yi taimako,
Ka ba da dukiya domin su zo.
A cece su daga halaka,
Su sami ceto da gafara.
Korus

Exit mobile version