Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 272 Ta da Ido, Ka Duba Gonaki Lyrics
1
Ta da ido, ka duba gonaki
Cikin duniyan nan yanzu,
Dukansu sun isa girbi,
Babu ma’aikata sosai.
KORUS
Ubangiji, muna roƙo,
Lokaci ‘na wucewa,
Nuna mana wurin aiki
Don mu kawo girbinka.
2
Tun da wuri sai mu tafi.
Ko da rana kada mu ƙi.
Ko gajiya ta zo da yamma,
Sai mu ƙarasa aikinmu.
Korus
3
Lalle za mu sha wahala
Cikin wasu gonaki.
Amma can a cikin Sama
Murna, murna za mu yi.
Korus