Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 271 Ba da Labarin Mutuwar Yesu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 271 Ba da Labarin Mutuwar Yesu Lyrics

 

1
Ba da labarin mutuwar Yesu,
Jini ya bayar domin cetonmu,
Amma ya tashi, ya ci nasara,
Ceto za a samu wurinsa kaɗai.

KORUS
Ba su labari, ba su labari,
Yawancinsu ba su ji ba.
Masu zunubi su tuba su bi shi,
Yesu Mai Cetonsu ne.

2
Ba da labari ga mazaje duk,
Ba za su tsira ba, sai dai sun ji.
Ba da labari a wurin mata,
Don su ma su tuba su ba da gaskiya.
Korus

3
Ba da labari don yara su ji,
Su ƙanƙanana su gane su bi.
Ko masu yawa, ko ɗaya kaɗai,
Mu ba su labari da ƙwazo sosai.
Korus

4
Ba da labari ga duk mutane,
Ko sun ji daɗi, ko wasu sun ƙi.
Yi ta addu’a da bangaskiya,
Maganarsa tana da iko sosai.
Korus

Exit mobile version