Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 270 Yesu Ɗan Allah Ne, Mai Ceton Duniya Lyrics
1
Yesu Ɗan Allah ne, Mai Ceton duniya,
Ya ƙaunace mu har ga mutuwa.
Wanda ya ba da gaskiya gare shi
Lalle ya tsira daga shari’a.
KORUS
Yesu mai iko duka ne,
Ba za ya kasa ba daɗai,
Sai mu kai bishara ko’ina a duniya
Shi kuwa za ya taimake mu.
2
Ƴanuwanmu sun ƃata cikin duhu,
Ba su da rai, ko sanin hanyarsa.
Kada su mutu cikin zunubansu,
Sai dai su zo su sami gafara.
Korus
3
Ubangijinmu za ya sake zuwa
Domin ya kai mu can a gidansa.
Me za mu ce idan mun ƙi biyayya?
Me za mu amsa masa ranan nan?
Korus
4
Sauri, jama’a, Yesu yana kiran
Duk Masu Bi su kama aikinsa.
Maza da mata duk da yara kuma,
Tashi, mu yi biyayya nandanan.
Korus
