Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 27 Yesu, Na Naɗa Ka A Cikin Zuciyata Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 27 Yesu, Na Naɗa Ka A Cikin Zuciyata Lyrics

 

1
Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata.
Ba wani iko ko’ina sai naka, Sarkina.
Kai yaro ne a da tare da mu ka sha
Jaraba, kai Mai Nasara, Yesu Mai Cetona.

2
Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata.
Ba wani wanda na ke so shi amshi mulkinta
Da zunubi kaɗai ya cika nawa rai,
Amma yanzu na sani kai Ubangijina ne.

3
Yesu, na naɗa ka, ban rage kome ba,
A bisa nawa duk da ni, sarauta za ka yi.
Da goshinka ya sha azabar naɗin ƙaya,
Yanzu ka ratsa mutuwa, ya kai Mai Nasara!

4
Yesu, an naɗa ka domin biyayyarka.
Suna mafifici aka ba mai mulkin mutuwa.
Yesu, ka cancanci ƙauna madauwamiya.
An naɗa ka! An naɗa ka tun da har abada!

5
Allah ya naɗa ka Ɗansa Maɗaukaki.
Baki ya kasa furtawa labarin girmanka.
Gare ka ɗaukaka har abada, Amin
An naɗa ka! An naɗa ka! Immanuel Almasihu.

Exit mobile version