Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 269 Zumuntar Masu Bi da Daɗi Kamar Me Lyrics
1
Zumuntar Masu Bi da daɗi kamar me!
Ba za a ga irinsa ba, sai can wurin Kristi.
2
Kadan wani Mai Bi ya je don wa’azi,
Kome nisan tafiyarsa, ba za mu manta ba.
3
Sai binsa za mu yi ta wurin roƙonmu.
Da ƙauna za mu raka shi, mu ƙarfafa shi kuwa.
4
Ko cikin ƙunci ne, ko wurin hatsari,
Ko ciwo ne, ko lafiya, ba za mu fasa ba.
5
Idan ya dawo fa, murnar da za mu yi
Ba za a ga irinta ba sai wurin Masu Bi.
6
Can wurin Yes dai inda ba rubuwa,
Can za mu gai da junanamu, mu gode har abada,
