Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 268 Yesu Ne Ya Ba Mu Suna, Mu da Mu Ke Binsa Nan Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 268 Yesu Ne Ya Ba Mu Suna, Mu da Mu Ke Binsa Nan Lyrics

 

1
Yesu ne ya ba mu suna, mu da mu ke binsa nan,
Yana ce da mu masuntan mutane.
Yana so mu yi ƙoƙari da mutanen duniya
Har mu jawo su gun Yesu Mai Ceto.

KORUS
Sai mu nemi ƴanu’wanmu,
Sai mu nemi ƴanuwanmu,
Sai mu nemi ƴanuwanmu
Har mu jawo su gun Yesu Mai Ceto.

2
Kamar ƃatattun tumaki ba su san gidansu ba,
Suna makuwa a cikin jeji kuwa.
Sai mu yi musu addu’a, mu yi musu shaida ma,
Har mu jawo su gun Yesu Mai Ceto.
Korus

3
Sai mu daɗa yin ƙoƙari, gama suna mutuwa,
Ba su san labarin ceton Allah ba.
Bar mu dinga faɗa musu har ya shiga zuciya,
Sai mu jawo su gun Yesu Mai Ceto.
Korus

Exit mobile version