Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 267 Ko Zan Tafi da Hannu Wofi Lyrics
1
Ko zan tafi da hannu wofi
Wurin Ubangijina?
Ba mai tuba da zan kawo
Ran da na ga fuskarsa?
[C1]
In na tafi da hannu wofi,
Babu kowa tare da ni,
Ran da na ga fuskar Yesu
Lalle kunya ce zan ji.
2
Ubangiji ya sha wahala
Garin neman tumaki,
Har ya ba da ransa duka
Ni Mai Bi fa, me zan yi?
3
Ƴanuwana ma sun tashi
Suna gama aikinsa.
Ga ni nan mai hannu wofi
Ni kuwa ban yi aiki ba.
4
Ni ma ina so in tashi
Cikin ƙarfin ikonsa,
Akwai mutane da yawa
Don sun kaunchi yesu.
