Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 266 Tashi, Mu Kama Aiki, Aikin Ubangiji Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 266 Tashi, Mu Kama Aiki, Aikin Ubangiji Lyrics

 

1
Tashi, mu kama aiki, aikin Ubangiji.
Hatsi ya isa girbi, zo dai, mu yi ta yi.
Ma’aikata sun kasa, girbi day awa ne.
Bari mu tara hatsi, kar ya lalace.

2
Tashi, mu sh iga yaƙi, yaƙin Ubangiji.
Yesu ya kira dukan ma su bangaskiya.
Shaiɗan da magautanmu suna ta tsayayya, Amma da ikon Yesu mā yi nasara.

3
Tashi, mu yi aniya, jin daɗi sai mu ƙi,
Ba ma wahalar banza cikin aikinsa.
Idan mun gama aiki, mun taru wurinsa,
Zai raba mana lada, ladan nasara.

Exit mobile version