Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 265 Muna Zuwa Wurin Yesu, Mai Ceto Lyrics
1
Muna zuwa wurin Yesu, Mai Ceto,
Don mu shiga aikinsa.
Shi ya kira mu mu yi ta wa’azi
Ko’ina a duniya.
KORUS
Yesu ne Shugaba,
Shi ne mai ƙaunar mutane.
Za mu taya shi nemansu
Don su sami gafara.
2
Komenene Yesu shi ya ce mu yi,
Za mu yi da zuciya ɗaya.
Za mu yi biyayya cikin abu duk,
Za mu yi ta wa’azi
Korus
3
Shi ya ce mu bar duk zunubai na dā,
Mu tafi da tsabtar rai.
Ko ya nemi kayan da ke wurinmu,
Za mu ba shi nandanan.
Korus
4
Sai mu yi aniya cikin aikinsa
Sai mu ƙara ƙoƙari.
Shi da kansa zai tafi tare da mu
Har iyakar duniya.
Korus
