Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 260 Yesu Ubangijinmu Ne, Shi Ne Sarkinmu Lyrics
1
Yesu Ubangijinmu ne, shi ne Sarkinmu,
Lalle shi ne zai yi mulkin dukan duniya.
KORUS
Yesu, Yesu, muna sonka domin ƙaunarka.
Kai kaɗai ka iya ceto, ceton gaskiya.
2
Muna so mu jawo mutane zuwa hanyarka,
Kada danginmu su mutu cikin zunubai.
Korus
3 Ku mutane, kasa kunne, sai ku tuba fa,
Sai ku bi Ubangijinmu, za ya cece ku.
Korus