Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 26 Ya Ubangijinmu Yesu, Tsare Mu da Daren Nan Lyrics
Ya Ubangijinmu Yesu,
Tsare mu da daren nan.
Kada kome ya same mu,
Rufe mu da hannunka.
Tun da farkon hasken safe
Kana nan tare da mu.
Ko da duhu ya rufe mu,
Kana wurin har yanzu.