Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 259 Muryar Makiyayi Ce Lyrics
1
Muryar Makiyayi ce
Can cikin jeji na ke ji,
Kira tumaki ƃatattu,
Nesa da garke sun watsu.
KORUS
Zo da su, zo da su,
Zo da su wurin cetonsu,
Zo da su, zo da su,
Zo da su wurin Yesu.
2
Wa za ya taimaki Yesu,
Taimake shi da samunsu?
Wa za ya kawo ƃatattu
Wurin da za a cece su?
Korus
3
Suna ta kuka can jeji,
Inda ba kowa a kan dutse.
Umarnin Yesu ka ke ji,
“Zo da tumakina yanzu.”
Korus