Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 258 Ga Masu Ɓacewa, Sai Ku Cece Su Lyrics
1
Ga masu bacewa, sai ku cece su,
Faɗaɗɗu, sai ku tsaishe su sosai.
Ruɗaɗɗu, batattu, bi su da kuka,
Kai su gun Yesu mai yawan tausayi.
KORUS
Bi masu ƃacewa, kada su mutu,
Kai su gun Yesu, mai yawan tausayi.
2
Yesu ya iya ya rayad da kowa,
Wanda ya kira, ba zai ƙi shi ba.
Bi su da ƙauna, ka kai su gare shi,
Ko za su karƃa, su yarda da shi?
Korus
3
Ceci mutane dai, Yesu ‘na jira.
Ku Masu binsa fa, me ku ke yi?
Kira mutane su juyo, su bi shi,
Yesu Ɗan Allah Mai Cetonsu ne.
Korus