Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 257 Ina da Aiki Nan, Allah Zan ɗaukaka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 257 Ina da Aiki Nan, Allah Zan ɗaukaka Lyrics

 

1
Ina da aiki nan, Allah zan ɗaukaka.
Raina zan sa a hannunsa a ƃoye a Sama can.

2
Zan yi ta aikina, zan cika kirana.
Da hannu biyu, da zuciya ɗaya in bauta wa Yesu.

3
Ya Ubangijina, ka ba ni Ruhunka.
Ka shirya bawanka a nan don aikin Sama can.

4
Ka ba ni taimako, ka ji addu’ata,
Don kada dai in kasa nan, in rasa ladana.

Exit mobile version