Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 255 Ina Gaskata da Yesu, Ubangijina Lyrics
1
Ina gaskata da Yesu, Ubangijina.
Bangaskiya ta kawo ceto cikakke.
2
Na gaskata gafararka, ga ni durƙushe,
Don ƙaunarka da jinƙanka, na amince.
3
Ina son ka tsarkake ni domin giciye.
Keƃe ni, ka tsarkake ni da jininka.
4
Ina roƙo ka bishe ni, Yesu, kai kaɗai.
Yau da gobe ka ke ba ni bukataina.
5
Ina gaskata ka, Yesu, ba zan kasa ba.
Na gaskata ka, Mai Ceto, har abada.