Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 254 Allahna, Ka Keƃe Ni, Tsarkake Ni Dominka Lyrics
1
Allahna, ka keƃe ni, tsarkake ni dominka.
Bari dukan kwanakina in yi ta yabonka.
2
Kebe hannuwana dai, su yi aikin ƙaunarka.
Bi da ƙafafuna kuwa har su tafi gun aikinka.
3
Bari muryata ta yi waƙar yabon Allahna.
Bari leƃunana su furta kullum saƙonka.
4
Nufina duk dukiyata sai ta zama dominka.
Iyawar da ka bayar sai in mayar don aikinka.
5
Na yarda duk nufina naka nufi ya aikata.
Zuciyata kuwa taka ce, za ta zama kursiyinka.
6 Ya Allah, ga ƙaunata tare da duk dukiyata.
Ina nan da shiri kuwa kullum domin bautarka,
