Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 253 Ya Allahna, Ƙarfafa ni Lyrics
1
Ya Allahna, ƙarfafa ni
Loton da duniya ta cuɗe,
Domin kullum in yabe ka, in yi nufinka
2
Ka buɗe mini idanu,
In ga kasawar ƴan Adam,
Idonka zai yi nasara, in yi nufinka.
3
Da hamdala da dangana,
Da ƴanci zan yi sujada,
Kullum in yi ta addu’a, in yi nufinka.
4
Ko’ina cikin ƃacin rai
Zan sa dangana gare ka,
Hikimarka ta bishe ni, in yi nufinka.
5
Da ikonka mai taimako,
Zan kiyaye wa’adina,
In manta da kaina, sai kai, in yi nufinka.
6
Algaitar Sama ta furta.
Su gaskatawa, da bege,
Da ƙauna sun yi nasara, in yi nufinka.
