Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 251 Yesu Mai Ceto ‘Na Kiran Duk Ƴan Ekklesiyarsa Lyrics
1
Yesu Mai Ceto ‘na kiran duk ƴan Ekklesiyarsa
Shi ne Magabaci namu, dukanmu masu binsa,
KORUS
Magabaci namu shi ne Ubangijinmu.
Za mu yi masa biyayya cikin kowane abu.
2
Wanda ya za daga bisa, bisanmu duka ya ke.
Kada mu bi nufin kanmu, sai mu bi nasa sosai,
Korus
3
In muna aiki a gida ka can a gona mu ke,
Kullum mu yi dukan kome cikin ikonsa kaɗai.
Korus
4
Nan gaba, ni a gare ni, rai shi ne Yesu Kristi
Har dukan k0wa ya gane Yesu ne Magabaci.
Korus
