Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 249 Ya Yesu Mai Ceto, Ka Ba Ni Sabon Rai Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 249 Ya Yesu Mai Ceto, Ka Ba Ni Sabon Rai Lyrics

 

1
Ya Yesu Mai Ceto, ka ba ni sabon rai,
Ka tsarkake ni da jininka, in ji, in bi sosai.

KORUS
Ka ba ni sabon rai, a cikin zuciyata.
Ka sauko nan da ikonka, ka ba ni sabon rai !

Ya Ruhu Mai Tsarki, farkad da ni yanzu
Daga nauyi, barci, ragwanci, ka wartsakad da ni.
Korus

3
Uba, ina roƙonka ka ba ni ƙishirwa
Ka shayar-da ni da ruwa mai rai, ka amsa kukana.
Korus

4
Yesu, Ruhu, Uba, na girmama ka yau.
Ka sauko nan da ikonka, na ba ka zuciyata.
Korus

5
Sai mu tashi fa ƴanuwa, mu yi ta yin addu’a
Mu yi shelar Yesu da cetonsa da ƙarfin zuciya.
Korus

Exit mobile version