Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 247 Ya Ubangiji, Mallake Ni Lyrics
1
Ya Ubangiji, mallake ni
Domin in zama da amfani.
Yi da ni yadda kai ka ke so,
Na cire hannu nawa yanzu.
2
Ya Ubangiji, maliake ni,
Kada in yarda da zunubi.
Bincike dukan zuciyata,
Wanke ni, Yesu, da jininka.
3
Ya Ubangiji, mallake ni,
Kai ne mai aika al’ajabi.
Zauna a cikin zuciyata,
Yi nufinka dai ta wurina.
4
Ya Ubangiji, mallake ni,
Ruhu Mai Tsarki ya cika ni.
Yi mulkin raina har za a ga
Halinka, Yesu, a wurina.