Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 245 Yi Nufinka Cikin Nawa Rai Lyrics
1
Yi nufinka cikin nawa rai,
Kai magini ne, ni yumbu ne,
Shirya ni bisa ga nufinka,
Na ba da kaina a hannunka.
2
Yi nufinka cikin nawa rai,
Gwada, ka gani yadda na ke,
Wanke ni sarai da jininka,
Na ba da kaina a hannunka.
3
Yi nufinka cikin nawa rai,
Ina da ciwo na zunubi,
Kai ne mai ikon warkad da ni,
Na ba da kaina a hannunka.
4
Yi nufinka cikin nawa rai,
Ka yi sarauta bisana dai.
Ba ni Ruhunka, kowa ya ga
Yesu ke zaune a zuciyata.
