Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 244 Ya Yesu Mai Cetona, Ga Ni Nan A Giciyenka Lyrics
1
Ya Yesu Mai Cetona, ga ni nan a giciyenka.
Ina neman ceto dai, ceto daga zunubi.
KORUS
Na dogara gare ka, Almasihu Ɗan Allah.
Kai kaɗai Mai Ceto ne, kai ka mutu domina.
2
Kai ne ka san zamana, kai kuwa ka san tashina
Cikin dukan aikina da tunanin zuciyata.
Korus
3
Kai ne ka ke kiwona, kai ne Makiyayina.
Cikin wannan duniya, kiyaye ni lafiya.
Korus
4
Almasihu Masoyi, zauna cikin zuciyata,
Cika ni da ƙaunarka, bar in bi ka, kai kaɗai.
Korus