Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 243 Ni Allahnka Ne, Ubangijinka Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 243 Ni Allahnka Ne, Ubangijinka Lyrics

Hymn 243 Ni Allahnka Ne, Ubangijinka Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 243 Ni Allahnka Ne, Ubangijinka Lyrics

 

1
Ni Allahnka ne, Ubangijinka,
Ba za ka shiga bautar wani ba.
Gare ni za ka dogara kaɗai,
Ni ma zan kiyaye ka zuwa rai

2
Ba za ka yi wa kanka sura ba,
Sura ta sama ko ta duniya.
Ba za ka yi musu sujada ba,
Ni, Ubangiji, za ka bauta wa.

3
Ba za ka ƃāta sunan Allah ba,
Ba za ka gama shi da ƙarya ba,
Amma a cikin duk bukatarka
Yi roƙo fa tare da godiya.

4
Ka tuna da rana mai tsarki,
Cikinta za ka daina aikinka.
Sai dai ka tuna da maganata,
Ka nemi ceton ƴanuwanka kuwa.

5
Uba da uwa za ka girmama,
Maganarsu ba za ka raina ba.
Biyayya za ka yi gare su kuwa,
Ni ma zan sa maka albarkata.

6
Kisa ba za ka yi shi ba lalle.
Ba za ka ɗauko fansa ba daɗai.
Ba za ka ƙi wanda ya ƙi ka ba,
Ƙaunarsa za ka yi har abada.

7
Zina da fasikanci za ka ƙi,
Kada ka ko yi tunaninsu fa.
Sai ka yi zamanka da tsabtar rai,
Kiyaye aurenka da tsarkin rai.

8
Kada ka yi sata ko yaudara.
Ba za ka ƙwace kayan kowa ba,
Amma ka yi aiki da hannunka,
Ka riƙa taimakon matsiyata.

9
Kada ka yi wa kowa shaidar zur.
Shaiɗan ne uban masu ƙarya,
Tsegumi da makirci nasa ne,
Dukansu dole za ka ƙi sosai.

10
Kada ka yi ƙyashin kayan mutum.
Kada ka nemi mata tasa kuwa.
Yi aikin ƙauna da makusanta,
Yadda kai ka ke so a yi maka.

Post navigation

Previous: Hymn 505 Oh Duniya Lyrics
Next: Hymn 493 Mutuwar Yesu Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version