Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 242 Dukan Sarautar Duniyan Nan Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 242 Dukan Sarautar Duniyan Nan Lyrics

 

1
Dukan sarautar duniyan nan,
Da ikonta da girmanta,
Game da kai, Mai Cetona,
Ba na maishe su kome fa.

2
Ƴanuwana da abokaina
Ba su da hanyar taimako,
Amma a bisa giciye
Yesu ya gama fansata.

3
I, jinin Yesu ne kaɗai
Wanda ya shafe laifina,
Mai yawan ƙauna hakanan,
Ba waninsa a duniyan nan.

4
Haƙuri, ƙauna, taimako,
Koyarwa, iko, gafara,
Zuciya mai tuba, ceto duk,
Shi Yesu ne mai bayarwa.

5
Ya Yesu Ubangijina,
Nan gaba bawanka na ke.
Zuciyata, raina, ƙaunata,
Na ba ka duka, naka ne.

Exit mobile version