Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 238 Ya Yesu, Ubangijinmu, Muna Roƙon Taimako Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 238 Ya Yesu, Ubangijinmu, Muna Roƙon Taimako Lyrics

 

1
Ya Yesu, Ubangijinmu,
Muna roƙon taimako,
Ga mu nan, mu marasa ƙarfi,
Sai ka shigo wurinmu.

KORUS
Zo yanzu, cika mu,
Yesu muna roƙonka.
Cika mu da naka iko,
Ba mu ƙarfin zuciya,

2
Ga mu nan a gaban kursiyin,
Muna jiran ikonka.
Ban da kai, ya Ubangiji,
Ba mu iya kome ba.
Korus

3
Ƴanuwanmu cikin duniya,
Ga su suna mutuwa.
Suna zaune cikin duhu,
Ba su san tafarki ba.
Korus

4
Ubangiji, muna roƙo,
Cika mu da ƙaunarka.
Bari Ruhunka ya ja mu,
Har mu cika aikinka.
Korus

Exit mobile version