Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 237 Bari nufin Mai Cetona Ya Bishe Ni Koyaushe Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 237 Bari nufin Mai Cetona Ya Bishe Ni Koyaushe Lyrics

 

1
Bari nufin Mai Cetona ya bishe ni koyaushe.
Da ƙaunarsa da ikonsa su mallake ni.

2
Kalmarsa ta zauna kullum cikin zuciyata sosai,
Don a rinjayi mugunta, sai ta ikonsa.

3
Salamar Allah Uban ta kiyaye duk raina,
Don in ta’azantar da su masu ƃacin rai.

4
Ƙaunar Yesu ta cika ni kamar cikowar teku,
Ya ɗaukaka, in ƙasƙanta, nasara ke nan.

5
Tsere gaba gaɗi zan yi, in tasar wa maƙiya,
Yesu shi zan duba kawai, cin gaba zan yi.

6
Jamalinsa ya haskaka loton neman ƃatattu,
Sanadin kuwa kar su damu, sai su gaskata.

Exit mobile version