Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 235 Kusa da Yesu Zan Riƙa Bi Lyrics
1
Kusa da Yesu zan riƙa bi,
Kullum in gami Ubangijina.
Loton bukata, a iske ni
Kusa da Yesu mai jin tausayi.
Kusa da Yesu mai jin tausayi.
2
Kusa da Yesu, ga hutawa
Daga zunubi da hukuncinsa.
Jini mai tsarki ya jawo ni
Kusa da Yesu Mai Cetona fa,
Kusa da Yesu Mai Cetona fa.
3
Kusa da Yesu har matuƙa,
Kowane aiki zan yi dominsa.
Can cikin Sama har abada
Kusa da Yesu zan yi zamana,
Kusa da Yesu zan yi zamana
