Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 233 Ya Almasihu, Kai Mai Ɗaukar Zunubai Lyrics
1
Ya Almasihu, kai mai ɗaukar zunubai,
Ba naka ba.
Duk na mutane ne, aza ba tasu ce,
A jikin gungume, wuya ka sha.
2
Addu’ata ka ji, roƙonka na ke yi
Don taimako.
Kada in goce kuwa daga kan hanyarka.
Ka tokare ni dai, Mai Cetona.
3
Tsoron me ni zan yi tun da ka riƙe ni
Da hannunka?
Mai Ceto, kai kaɗai an haɗa ni da kai,
Tsayad da ni sosai, ni naka ne.