Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 230 Albarka Tana Kan Mutum Wanda Bai Ratse Ba Lyrics
1
Albarka tana kan mutum wanda bai ratse ba,
Wanda bai tsaya a hanya ta masu zunubi ba.
2
A wurin masu ba’a, shi ba ya kan zauna ba,
Maganar Allah ya ke bi dare da rana kuwa.
3
Misalin itace ne shi a bakin ruwaye,
Zai ba da ƴaƴa lotonsa, yaushi kuwa ba ya yi.
4
Duk aikinsa da ya ke yi, albarka tana kai.
Miyagu kamar ƙaiƙai ne, iska zai ture su.
5
Ranar shari’a, miyagu ba za su tsaya ba,
Ko kuwa su masu zunubi a gidan adalai.
6
Ubangijinmu kuwa ya san tafiyar adalai.
Amma tafarkin miyagu lalle zai lalace.
